Home Labarai An tsare mawaƙi Ice Prince bisa zargin guduwa da ɗan sanda

An tsare mawaƙi Ice Prince bisa zargin guduwa da ɗan sanda

0
An tsare mawaƙi Ice Prince bisa zargin guduwa da ɗan sanda

 

 

An kama wani mawakin zamani na Nijeriya, Ice Prince Zamani bisa zargin guduwa da ɗan sanda.

Kakakin rundunar ƴan sandan na jihar Legas, Ben Hundeyin ya tabbatar da hakan a yauJuma’a.

Hundeyin ya bayyana lamarin da ya kai ga kama Ice Prince a shafin sa na Twitter.

Ya ce “Da karfe 3 na safiyar yau, an tayar da @Iceprincezamani saboda tukin mota ba tare da lasisi ba.

“Sai ya amince a kai shi Caji-ofis. Daga nan ne kuma ya yi awon gaba da ɗan sandan da ke cikin motarsa, inda ya kai masa hari tare da yi masa barazanar jefa shi a cikin kogi.

“An kama shi kuma za a gurfanar da shi a yau,” Hundeyin ya rubuta.

Ice Prince ya yi suna bayan ya fito da waƙar “Oleku”, ɗaya daga cikin wakokin da aka fi yin mai-mai ɗin su a tarihi a Najeriya. Ya kuma ci kyautar girma ta 2009 Hennessy Artistry Club Tour.