Home Ƙasashen waje TSAUTSAYI: Ɗan sanda ya harbe yarinya yayin kama mai laifi

TSAUTSAYI: Ɗan sanda ya harbe yarinya yayin kama mai laifi

0
TSAUTSAYI: Ɗan sanda ya harbe yarinya yayin kama mai laifi

 

A jiya Juma’a ne dai ƴan sanda a Jihar Los Angeles da ke Amurka su ka tabbatar da mutuwar wata yarinya ƴar shekara 14 bayan da harsashi ya fice ya kuma same ta yayin da ƴan sanda su ka zo kamen wani mai laifi a kantin sayar da kaya.

A wata sanarwar da rundunar ƴan sandan ta fitar, ta ce ta samu rahoton cewa wani mutum ɗauke da bindiga ya kai hari kantin, kuma bayan da jami’an ƴan sanda su ka iso wajen, sai su ka tarar kowa a kwance a kantin.

A cewar sanarwar, ƴan sandan su na zuwa ba su yi wata-wata ba sai su ka buɗewa mai laifin wuta su ka kuma kai shi caji-ofis.

A she su ƴan sandan ba su san cewa sun bar baya da ƙura ba, bayan da ashe harbin da su ka yi, harsashi ya fasa bango Ya kuma samu yarinyar tana ɗakin gwada kaya.

Nan take dai mai laifin ya ce ga garinku nan ka da a ka bincika jikinsa, sai ba a samu bindigar da a ka ce ya na da shi ba.

“Ashe su ƴan sandan ba su san cewa akwai yarinya a bayan mai laifi ba ta cikin dakin gwada kaya tare da mahaifiyar ta.

“A she lokacin da a ke harbe-harben nan harsashi ya same ta, inda itama ta rasu nan take,” inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma kara da cewa harsashin ya raunata wata mata kuma tuni a ka kai ta asibiti.