Home Ƙasashen waje Tsawa ta hallaka mutane 21 a Indiya

Tsawa ta hallaka mutane 21 a Indiya

0
Tsawa ta hallaka mutane 21 a Indiya

 

 

A ƙalla mutane 21 ne su ka mutu a jihar Bihar da ke gabashin kasar Indiya, sakamakon tsawa da walkiya a cikin ruwan sama da a ka kwashe sa’o’i a na maka wa.

Wani jami’in hukumar kula da ibtila’i ta jihar a jiya Talata ya bayyana cewa, waɗanda suka mutu manoma ne ko ma’aikata a gonakin da su ke tsaka da shuka amfanin gona ko kuma wasu ayyukan na noma.

A cewar jami’in, an samu rahoton mutuwar mutane kusan gundumomi 10 a jihar.

Jami’in ya kara da cewa, Purnia da Araria dukkansu sun bayar da rahoton mutuwar mutane huɗu, uku sun mutu a gundumar Supaul, inda a ka bayar da rahoton mutuwar biyu daga Banka, Jamui da Nawada, sai kuma mutum ɗaya ya mutu a Begusarai, Sheikhpura, Saran da Saharsa.

Babban Ministan Bihar, Nitish Kumar ya ba da sanarwar biyan diyya na kudi Rupees ɗin Indiya 400,000 kwatankwacin dalar Amurka 5,023 ga kowane dangin da mutuwar ta shafa.

Babban Ministan ya shawarci jama’a da su kasance cikin shiri a lokacin da ake cikin yanayi maras daɗi.