Home Labarai Tsawa ta kashe yarinya ƴar shekara 12 a Jigawa

Tsawa ta kashe yarinya ƴar shekara 12 a Jigawa

0
Tsawa ta kashe yarinya ƴar shekara 12 a Jigawa

 

Rahotanni a jihar Jigawa na nuni da cewa tsawa ta kashe wata yarinya ƴar shekara 12, mai suna Maryam Rabi’u Garba sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a Ƙaramar Hukumar Kaugama ta jihar.

Wani mazaunin garin ya shaidawa DAILY POST cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, a lokacin da yarinyar ta fake a cikin wani aji a wata makaranta sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Ya ce yarinyar na kan hanyarta ta koma wa gida ne bayan mahaifiyarta ta aike ta.

Kakakin rundunar ƴan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya yi sanadin mutuwar yarinyar mai suna Maryam Garba mai shekaru 12 a garin Kaugama.

Ya ce an garzaya da yarinyar asibiti kuma likita ya tabbatar da rasuwarta.