
Majalisar Dokokin Jihar Oyo, ta tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Rauf Olaniyan daga mukaminsa, a safiyar yau Litinin.
Majajlisar ta tsige mataimakin gwamnan ne bisa shawarar kwamitin mutum bakwai da Babban Jojin Jihar, Mai Shari’a Munta Abimbola ya kafa domin bincikar shi kan aikata ba daidai ba.
Ɗaukacin mambobi 23 da ke majalisar sun amince da tsigewar, wacce ta fara aiki nan take.
Rahoton da kwamitin ya gabatar wa majalisar a yau Litinin ya ce, an samu Olaniyan da aikata duk laifuka uku da ake zargin shi da su.