
An gano wani yaro dan shekara 3 mai suna Olamide Taiwo da aka yi gudu da shi a cikin motar mahaifinsa da aka sace a garin Owode-Oniri da ke Ikorodu a jihar Legas.
City and Crime ta ruwaito cewa yaron na cikin motar mahaifinsa ne lokacin da wasu da ake zargin barayi ne suka sace motar suka kuma gudu da ita a Ikenne, jihar Ogun, a ranar Asabar.
Mahaifin, mai suna Taiwo Fayobi, ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa an sace motarsa kirar Toyota Camry mai lamba PKA 446GV a lokacin da ya sauko daga motar domin ya bude kofar gidansa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yan sanda Omolola Odutola, ya bayyana cewa an sace motar ne lokacin da Fayobi ya sauko zai bude kofarsa lokacin da take.
Da ta ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ‘yan sanda Omolola Odutola, ya bayyana cewa motar da injinta ke aiki, an sace motar ne lokacin da Fayobi ya sauko ya bude kofarsa.
“Wani Taiwo Fayobi da ke zaune a Ikenne Jihar Ogun ya kawo rahoton cewa ya taso ne da motarsa kirar Toyota Camry PKA 446 GV domin bude kofarsa, wasu barayi guda biyu ne suka gudu da motarsa, tare da yaronsa dan shekara uku a ciki.
Daga baya Odutola ya shaidawa manema labarai a Abeokuta cewa wani mutum ne ya gano yaron a jihar Legas.
Ta bayyana cewa an gano yaron an manna masa alama da aka rubuta “Ikenne” a jikin sa.
Odutola, ta ce ba a gano motar da aka sace ba har yanzu.