
Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ƴan shekarar 1992 sun ci alwashin ɗorewa da bada tallafin naira miliyan 1 a kowacce shekara ga ɗalibai ƴan asalin Jihar Kano.
Ƙungiyar ta fara bada wannan tallafi ne sama da shekaru biyar da su ka gabata.
Bayan tallafin karatun, ƙungiyar kuma na bada wasu taimakon ga ɗalibai da ma jami’ar baki ɗaya a duk lokacin da ta ke yin taron sada zumunci a duk shekara.
Shugaban ƙungiyar, Ɗahiru Sa’id, yayin da ya ke jawabi a taron sada zumunci na bana, karo na 6 kenan, ya ce tallafin karatun wani ɓangare ne na taimakon da su ke bayarwa.
Ya ce “ƙungiyar ta samu nasarori da dama, da su ka haɗa da tallafin karatu na Naira miliyan 1 duk shekara ga ɗalibai ƴan asalin jihar Kano, marasa ƙarfi domin su samu damar biyan kuɗin makaranta.
“Haka kuma mu na tallafawa iyalan waɗanda su ka rasu a cikin mu. Mu na kuma fitar da ɗaurararru da ga gidajen yari da kuma kai ziyara zuwa gidajen marayu.
“mun kuma tallafawa waɗanda su ka samu ibtila’in ambaliyar ruwa, sannan mu na taimakawa marasa lafiya ƴan jihar Kano a asibitoci a faɗin jihar. Sannan kuma muna tallafawa junan mu idan ɗayan mu zai yi aure ko suna da sauran bukukuwa,” in ji Sa’id.
Ya kuma ƙara da cewa tun sanda a ka kafa ƙungiyar a 2016, ba ta taɓa gajiyawa wajen taimakon da yanke bayarwa ba, duk da halin da tattalin arziƙi ya faɗa sakamakon annobar korona.
Tun da fari dai ƙungiyar, a bisa jagorancin Farfesa Hajara Sanda, ta miƙa cekin naira miliyan 1 ga Shuagaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas a ranar Juma’a.
Da ya ke jawabi bayan karɓar cekin kuɗin, Farfesa Abbas ya yabawa ƙungiyar, in da kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai da su kwaikwayi irin aiyukan alherin da ƴan shekarar 1992 ɗin ke yi.