Home Labarai Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

0
Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a karkashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazabar Shema, karamar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama dan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Radda da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheka.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane dan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Radda, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya mika katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.