Home Labarai Tsohon kakakin Ibrahim Badamasi Babangida, Duro Onabule ya rasu

Tsohon kakakin Ibrahim Badamasi Babangida, Duro Onabule ya rasu

0
Tsohon kakakin Ibrahim Badamasi Babangida, Duro Onabule ya rasu

 

Cif Duro Onabule, tsohon dan jarida kuma tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badsmasi Babangida ya rasu.

Onabule, a cewar wani makusancinsa, Eric Teniola, ya rasu a jiya Talata yana da shekaru 83 a duniya.

“Cif Duro Onabule ya mutu da yammacin yau,” wata majiya ta iyali ta shaida wa jaridar The Guardian.

Kawo yanzu dai ba a san musabbabin mutuwarsa ba.

An haifi Onabule a garin Ijebu-Ode, jihar Ogun, a ranar 27 ga Satumba, 1939.

Ya halarci Makarantar Grammar CMS da Makarantar Aikin Jarida, London.