
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Kano, Sadiq Wali, ya samu nasarar lashe zaben fidda gwanin takarar gwamna na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Sani Abacha Youth Center, Madobi Road, Kano.
Wali dai ɗan tsohon Ministan Harkokin Waje ne, Ambasada Aminu Wali.
Da yake bayyana sakamakon zaben da safiyar Alhamis, shugaban kwamitin zaben, Bunmi Adu, ya ce Sadiq Wali ya samu kuri’u 455, inda ya doke abokin hamayyarsa na kusa-kusa Ibrahim Ali-Amin wanda ya zo na biyu da kuri’u 333.
Tsohon shugaban ma’aikata na tsohon Gwamna Rabi’u Kwankwaso, Yunusa Dangwani, ya zo na uku bayan ya samu kuri’u 276, yayin da Yusuf Dambatta, tsohon kwamishinan ƙasa da tsare-tsare ya samu kuri’u 182 inda ya samu matsayi na hudu.
Tsohon kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa, Muaz Magaji da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji, ya samu kuri’u 25 kowannen su, yayin da Mustapha Bala Getso ya samu kuri’u 20.
Ƴan takara shida ne suka fafata a zaben fidda-gwanin yayin da sauran ƴan takara biyu, Mohammed Abacha da Jafar Sani Bello suka shiga zaben fidda-gwanin da aka yi a karkashin jagorancin Shehu Sagagi.