
Ƙasa da makonni biyu da ya sanar da ficewar sa da ga jam’iya mai mulki ta APC, tsohon mashawarci ga Gwamnan Jihar Kano kan harkokin yada labarai , Salihu Tanko Yakasai ya kuma sanar da komawar sa cikin jam’iyyar PRP.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Kano, Yakasai, wanda ake yi wa laƙabi da Dawisu, ya ce ya koma jam’iyyar PRP ne domin ita ce ya ke da yaƙinin za ta iya sauke nauyin da al’umma za su ɗora mata, sakamakon kyawawan manufofinta.
A sanarwar, wacce ya sanya wa hannu, Yakasai ya ce “Na shiga siyasa shekaru ashirin da biyu da suka wuce da tunanin cewa akida da siyasar yanci sune zasu zama ginshikin siyasar mu, kuma wannan ce ta sa na hada kai da wadanda nake tunanin suma wannan ne tunanin su. Na bi su sau da kafa, bisa ladabi da biyayya. Hakan ta sa nai ta tsalle daga wannan jam’iyar zuwa wata. Na fara da APP wadda ta koma ANPP, sannan muka shiga CPC daga karshe muka kare a APC.
“Bayan ficewa ta daga APC, Alhamdulilah zan iya cewa yanzu nima gashin kai na nake ci! Na tsaya da kafa ta, kuma ina da yancin fadar ra’ayi na kai tsaye ba tare da shayi ba. Yanci kuma shine gishirin rayuwa, musamman a siyasance, ba abinda ya kai yanci muhimmanci a siyasan ce.
“Na dade ina shaawar jam’iyar PRP saboda akidar ta, da jajircewar ta, duk da matsalolin da suke addabar siyasar wannan zamanin, haka kuma na dade ina shaawar tarihin ta. Ganawa da nayi da wasu daga cikin jagororin ta, ya na daya daga cikin abubuwan da suka sa na yanke shawarar shiga jam’iyar PRP. Bayan adduah, shawarwari, da tuntuba, shi yasa na yanke shawarar shiga jam’iyar PRP Nasara, jam’iyar mu ta gado, ta kaka da kakanni, jam’iyar talakawa!,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “A wannan gwagwarmayar, hawa katanga ba namu bane, ihu bayan hari ba abin yi bane, sannan mu yi ta suka ba ma shiga ana damawa da mu ba zai kawo mana chanjin da muke raji ba. Dole sai mun tsunduma cikin harkar nan tsundum, sannan zamu iya kawo chanji, mu cika burin magabatan mu na ganin kasar mu ta ci gaba domin kannen mu, da ‘ya’yan mu da jikokin mu har ma da wanda za’a haifa can gaba.
“Dan haka nake kira ga yan’uwa na matasa, maza da mata, da su zo mu shiga jam’iyar PRP. Jam’iyar Mallam Balarabe Musa, da Abubakar Rimi, da kuma Mallam Aminu Kano. Wannan jam’iyar Mallam Balarabe Musa ya rike ta tsahon ran sa, inda ya raya ta har ta kawo yanzu bayan rasuwar na gaba da shi. Sannan bayan shi, yanzu aka samu wanda suka ci gaba da jan akalar shugabancin ta, domin raya ta. Dukkan su burin su kenan, jam’iyar nan ta rayu bayan su, ta kuma zo kan mu domin mu ci gaba da raya ta har jikokin mu”
“Wannan gwagwarmayar yau ta mu ce, kuma dole mu rungume ta hannu bi-biyu da kauna da kishi, da jajircewa da rashin tsoro. Kuma ina fatan yan’uwa da abokai na zasu shigo ta, domin mu ci gaba da raya ta, mu zamanantar da ita, mu kuma tabbatar ta kafa mulki domin cimma burin wanda suka kafa ta na ganin an gyara kasar nan. Ba mu da wani zabi da ya wuce PRP, ita ce zata bamu damar gyara kasar nan da Izinin Allah.
“Da ni, da sauran yan’uwa na daga jihohi daban daban da muka shiga jam’iyar PRP a yau, babban abinda yake gaban mu na farko shine kokarin ganin mun dinke jam’iyar ta zama daya, mu kuma zamanantar da ita domin ya zamanto zata iya gogayya da kowacce jam’iya a Afirka ma ba Najeriya ba, domin samar da gwamnati ingantacciya ta gari, mai kishin al’ummar ta. Dinkakkiyar jam’iyar PRP ina da yakinin zata iya lashe duk wani zabe a kasar nan, musamman ma a Arewa inda nan ne cibiyar ta. Ina godewa wadanda suke rike mana jam’iyar PRP Nasara, bisa namijin kokarin da suka yi,”