
Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya mayar da takardun sa na tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Atiku Abubakar yana daga cikin na gaba gaba wajen neman takarar Shugaban Kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP mai adawa.
Atiku dai yanjima yana son zama Shugaban Najeriya tun a shekarar 1993. Yayi takara a shekarar 2007 da kuma 2011 da 2015 dukkansu yana shan Kaye a zaben fidda gwani a hannun tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.