
Tsohon Ministan Wasanni da Ci-gaban matasa, Solomon Dalung, a jiya Alhamis ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai.
Dalung, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya fito takarar a jam’iyyar Social Democratic Party, SDP.
Ɗan Jihar Plateau, Dalung ya rike mukamin minista a tsakanin 2015 zuwa 2019, wa’adin farko na shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sanarwar na majalisar ta biyo bayan ficewar sa daga jam’iyyar APC mai mulki a ranar 18 ga watan Afrilu.
“Masu hikima, waɗanda suka ƙi yin mulki, to su shirya shan wahalar mulkin wawaye,” Socrates.
“Da yardar Allah zan karbi fom na tsayawa takara a mazabar majalisar wakilai ta Langtang ta arewa da ta kudu,” in ji Dalung.
Ya ce zai karbi fom din tsayawa takara na SDP a yau Juma’a, a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa da ke Abuja.