Home Siyasa Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ya fice daga APC zuwa PDP

Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ya fice daga APC zuwa PDP

0
Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa ya fice daga APC zuwa PDP

 

 

Mustapha Inuwa, tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, SSG, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Inuwa, wanda ya sha kaye a yunkurinsa na neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya bayyana sauya shekar ta sa zuwa PDP ne a yau Lahadi a Katsina, yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa.

Ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan tattaunabwa da magoya bayansa a fadin jihar

Inuwa wanda ya yi aiki a matsayin SSG a gwamnatin Gwamna Aminu Masari daga 2015 har zuwa zaben fidda gwani na gwamna a watan Mayun 2022, ya yi ikirarin cewa an mayar da shi saniyar-ware a duk harkokin APC a jihar.

“Idan za a iya tunawa, a lokacin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC a jihar, mun san duk abin da ya faru a wancan lokacin, kuma a karshe an bayyana wanda ya yi nasara.

“Mun amince da shan kaye kuma mun yi alkawarin mara wa dan takarar jam’iyyar baya, bayan da ya ziyarce ni kuma na ba shi tabbacin goyon bayan da ya dace.

“Amma abin takaici, tun a wancan lokacin, ba a taba tuntuɓa ta da wata harka da ta shafi ci gaban jam’iyyar a jihar Katsina ba, wanda hakan ya sa a ka maishe mu saniyar-ware a jam’iyyar.

“Wannan alama ce karara cewa ba a ɗaukar mu a matsayin cikakkun ƴan APC, bar ta kai ga wasu ma na cewa za su iya cin zabe ko ba mu.

“Duba da wannan yanayi, mun gamsu cewa ba za mu iya jure zama a haka ba. Sabo da haka Ni da ɗaukacin magoya baya na mun sauya sheƙa zuwa PDP,” in ji shi.