Home Labarai Tsohon shugaban jami’ar ABU, Farfesa Mahdi ya rasu

Tsohon shugaban jami’ar ABU, Farfesa Mahdi ya rasu

0
Tsohon shugaban jami’ar ABU, Farfesa Mahdi ya rasu

Tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello Zaria, ABU, Farfesa Abdullahi Mahadi ya rasu, ya na da shekaru 77.

Shahararren masanin tarihi da samun nasararori a fannin ilimi, marigayin ya taba rike mukamin shugaban jami’ar jihar Gombe, da jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Gombe.

Ya fara aikin koyarwa a shekarar 1984 a matsayin babban malami a fannin tarihi a ABU inda likkafarsa ta ci gaba zuwa mataimakin shugaban jami’a tsakanin 1998 zuwa 2004.

Marigayi farfesa ya kasance wanda ya samu lambar yabo ta kasa ta CON.

A cewar jaridar The Abusite, marigayin ya samu lambar yabo ne a Cibiyar Ilimi, Kimiyya da Al’adu ta Islama, hedkwatar ISESCO, Rabat, Maroko a cikin 2017 da ga Masarautar Saudi Arabiya a kan “Kula da da Muhalli da Kariya a Duniyar Musulunci”.

Ya wallafa da kuma wallafawar haɗin gwiwa na littattafai da dama, daga cikinsu akwai Tarihin Najeriya don Makarantu da Kwalejoji, Littattafai I-II, (Longman, 1988).