
Tsohon ɗan takarar gwamna kuma ɗan jam’iyyar APC, Bashir I. Bashir ya fice daga jam’iyar me mulki a Jihar Kano.
A wasiƙa da ya rubuta wa ciyaman ɗin jam’iyar na mazaɓar Alawa a Karamar Hukumar Gaya, Bashir ya godewa ciyaman ɗin bisa goyon baya da haɗin kai da ya ke bashi.
Sai dsi kuma Bashir bai faɗi jam’iyyar da zai koma ba, inda ya shaida wa ƴan jarida cewa nan gaba kaɗan zai samar da jam’iyar da zai koma.
Bashir, wanda injiniya ne shi, ya tsaya takarar gwamna a jam’iyar PDM, sannan kuma a baya abokin siyasar tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ne.