
A yau Lahadi ne tsohuwar jaruma a masana’antar fim ta Kannywood, Hannatu Umar Sani ta rasu.
Mujallar Fim ta rawaito cewa Hannatu ta rasu a gidan yayar ta da ke unguwar Katampe a garin Abuja.
Wata majiya a gidan nasu ta shaida wa Mujallar Fim cewa Hannatu ta tashi lafiya ƙalau yau da safe, amma bayan ta fito za ta je falo ta karya kumallo, sai ta yanke jiki ta faɗi, inda da aka zo kanta, tuni rai ta yi halin sa.
Majiyar ta ce an yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.
Allah ya jiƙan ta da rahama, amin.