Home Siyasa Tun makonni 4 da su ka gabata maganar haɗewar Kwankwaso da Obi ta watse

Tun makonni 4 da su ka gabata maganar haɗewar Kwankwaso da Obi ta watse

0
Tun makonni 4 da su ka gabata maganar haɗewar Kwankwaso da Obi ta watse

 

 

Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Doyin Okupe, ya ce an kawo ƙarshen yunƙurin da ake yi na haɗewa tsakanin jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP da ta Peter Obi wato LP.

Yayin wani shirin siyasa na kafar talabijin din Channels jiya Talata Mista Okupe ya ce tun kusan makwanni hudu da suka gabata aka kawo ƙarshen yunƙurin, amma sai ƴan jam’iyyar NNPP suka ci gaba da yaɗa farfaganda a kan batun dn ganin sun raɓa kansu da farin jinin da Mista Obi ke da shi a wajen yan Najeriya.

Ya ce Kwankwaso ya ki amincewa ya zama mataimakin shugaban ƙasa ga Obi ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili da ya wuce saboda shi dan arewa ne ba.

”Ni na jagoranci ɓangarenmu na LP a wannan tattaunawa, daga lokacin da na nuna musu cewa yanzu lokaci ne da ya kamata a mika mulki ga yankin kudancin Najeriya amma suka ƙi amincewa muka nuna sasantawar ba za ta yiwu ba” in ji Mista Okupe.