
Tsohon mataimakin Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana cewar, shi ba yana son zama Shugaban Najeriya bane ko ta halin yaya kamar yadda wasu ke fassara shi.
Alhaji Atiku Abubakar ya shaidawa sashin Hausa na BBC cewar, shi baa yana son zama Shugaban kasa bane ko ana muzuru ana shaho, yace da haka ne kudurinsa, da bai janyewa Mashood Abiola ba a shekarar 1992.
A cewarsa, ya janyewa tsohon mai gidansa, Olushegun Obasanjo, a lokacin da dukkan Gwamnonin Najeriya suka amince masa tsayawa takara Shugabancin Najeriya a shekarar 2003.
Mai neman jam’iyyar PDP ta tsayarda shi takarar Shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya kara da cewar, tunda yake sau daya ya taba yin takarar Shugaban kasa a tsawon rayuwarsa.
“Ba ko a mutu ko ai rai nake neman zama Shugaban Najeriya ba. A shekarar 1992 na janyewa Abiola ya tsaya takara. Haka nan kuma, a 2003 lokacin da dukkan Gwamnoni suka goyi bayan na tsaya takara na hakura na barwa Obasanjo domin yayi wa’adi na biyu”
“A shekarar 2007 na yi takarar Shugaban kasa, duk kuwa da cewar Obasanjo bayan son na yi wannan takara. Duba da wannan tarihi, zaku faahimci cewar sau daya ne tak na taba yin takarar Shugaban kasa. Wannan kuma yake nuna ba ko ana muzuru ana shaho nake nema ba”
Alhaji Atiku Abubakar, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar mai mulki a Najeriya ta APC zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, yace yana son zama Shugaban kasa ne domin sanya kasarnan akan gwadabe na gaskiya na tattalin arziki.
A cewarsa, a zamansa mataimakin Shugaban kasa na tsawon shekaru 8, ya san hanyoyi da yawa da za’a magance matsalolin da suke damun wannan kasa, yace zai iya fitar da wannan kasa daga halin da take ciki ne kadai idan ya zama Shugaban kasa.
“Idan ‘yan Najeriya suka bani dama a matsayin Shugaban kasa, zan janyo masu zuba jari daga kasashen duniya,domin dakile matsalar kudaden musaya da ake fama da ita da kuma karancinsu a babban bankin Najeriya”
“Ba zaka iya janyo masu zuba jari a Najeriya ba, idan kwai gibi ta wajen samun kudaden musaya. Amma ni zan yi kokari naga na samar da tsarin da zai sanya kudaden kasashen waje da ake musaya da su su zama suna samuwa cikin sauki”
“Duk da cewar wannan Gwamnatin tana kokarin ganin ta janyo masu zuba jari a Najeriya, amma kuma bata share musu wata hanya ba da yake nuna zasu zo da kudadensu domin yin kasuwanci a Najeriya ba tare da wata gargada ba”
“A matsayina na wanda yake da kamfanoni, ina da kwarewa akan yadda zan samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya. Matasa zasu samu dama sosai ta samun aikin yi indai na zama Shugaban kasa” A cewar Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar.