Home Labarai Tur da kalaman Kwankwasokan auren ‘yar Ganduje – Gwamnatin Kano

Tur da kalaman Kwankwasokan auren ‘yar Ganduje – Gwamnatin Kano

0
Tur da kalaman Kwankwasokan auren ‘yar Ganduje – Gwamnatin Kano
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin Kano ta yi tur da kalaman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kan kiran auren ‘yar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da yayi da sunan auren bazawara, wanda aka yi a makon da ya wuce a jihar Kano.

A ranar Asabar da ta gabata ne Shugaban kasa da Gwamnoni da manyan attajirai suka yi tururuwar zuwa jihar Kano domin shaida auren ‘yar Gwamnan Kano Fatima Ganduje da dan gidan Gwamnan jihar Oyo, Idris Ajimobi.

A cewar Gwamnatin Kano, ta bakin Kakakin Gwamnati kuma kwamishinan yada labarai Malam Muhammad garba, ya bayyana cewar, Gwamnati ta aikawa Sanata Kwankwaso gayyatar daurin auren, amma bai amsa gayyatar ba,maimakon yayi adduah sa ya dinga kalaman batanci.

“Sambamu ji dadin kalaman tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ba na kiran wannan aure na fatima Ganduje da sunan auren zawarawa, wannan bai dace ace mutum kamar Sanata Kwankwaso yayi irin wannan kalamai”

“Gwamnati tayi tur da irin wadannan kalamai na rashin girmammawa da Sanata Kwankwaso yayi, a matsayinsa na uba, ya kamata ace yayi adduah da fatan alheri ba wai bita da kulli ko habaici da bakar magana ba” A cewar Muhammad Garba.

Bayan an daurin auren ne, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shaidawa taron magoya bayansa a Kaduna cewar, sabida auren zawarawa aka toshe hanyoyin shiga na Kano gabas da yamma,kudu da Arewa sabida kawai auren zawarawa guda daya. A cewar Sanata rabiu Musa kwankwaso.