
Daga Hassan Y.A. Malik
Wani mutum mai shekara 64 da dansa mai shekara 19 sun gurfana a gaban kotun majistare ta Katsina a bisa zarginsu da yi wa ‘yar makwabcinsu mai shekara 9 fyade.
Sunan mutumin Lawal Angala yayin da dan kuma ya ke amsa Isah.
Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Sani Ado, ya fada wa kotun cewa wadanda ake zargin mazauna garin Safana ne a jahar Katsina, kuma sun aikata wannan laifi a ranar 2 ga watan Mayu.
Ya ce mahaifiyar yarinyar, Shamsiyya Abdullahi ita ta kawo rahoton aukuwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Safana.
A cewar shi, “Wadanda ake zargin sun shigar da yarinyar ne cikin dakin Angala, inda suka yi lalata da ita.”
Sufeto Sani ya kara da cewa a yanzu haka uban da dan shi na fuskantar tuhumar aikata fyade, laifin da ya saba wa dokar “Penal Code”.
Alkalin kotun, Hajiya Dikko ta ce za a iya yanke musu hukunci ne kawai a babbar kotu, amma ta daga sauraran karar zuwa ranar 14 ga watan Yuni.