Home Siyasa Uba Sani na APC ya lashe zaɓen gwamna na Kaduna

Uba Sani na APC ya lashe zaɓen gwamna na Kaduna

0
Uba Sani na APC ya lashe zaɓen gwamna na Kaduna

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Uba Sani, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kaduna a zaɓen 2023.

Jami’in da ya sanar da sakamakon zaɓen, Farfesa Lawal Suleiman Bilbis ya ce Sani ya samu kuri’u dubu 730,002 inda ya doke abokin takararsa, Isa Ashiru na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u dubu 719,196.

Bilbis, wanda shi ne mataimakin shugaban jami’ar Usmanu Dan Fodio da ke Sakkwato, ya ce dan takarar jam’iyyar Labour, Jonathan Asake, ya zo na uku bayan ya samu kuri’u dubu 58,283.

Ya kara da cewa dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Suleiman Hunkuyi, ya samu kuri’u dubu 21,405 inda ya zama na hudu a zaɓen.