
Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya zaɓi Hadiza Sabuwa Balarabe, Mataimakiyar Gwamna Nasir El-Rufa’i a matsayin abokiyar takararsa a zaɓen 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Uba Sani ya fitar a jiya Litinin.
“Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kaduna, ina mai farin cikin sanar da cewa na zaɓi mai girma mataimakiyar Gwamna, Dokta Hadeeza Balarabe a matsayin abokiyar takarata a zaben gwamna na 2023 a jihar Kaduna,” in ji sanarwar.
“Dakta Hadiza Balarabe ta ba da gudunmawa sosai ga gagarumin ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a jihar.
“Dakta Balarabe ta nuna kwazo sosai wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na mataimakiyar Gwamna wanda ya kara mata daraja a cikin masu ruwa da tsaki a jihar,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Don haka ina kira ga al’ummar jihar Kaduna da su goyi bayan zabin Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe a matsayin abokiyar takarata.
“Na kuma bukace ku da ku fito ranar zabe don kada mana kuri’a yayin babban zaben 2023 mai zuwa. Zabar mu a 2023 zai ba mu damar gina jihar Kaduna cikin lumana, wadata, da kuma girma,”