
A yau Laraba ne wani ƙudirin doka na kafa Jami’ar Ilimi da Fasaha ta Tarayya a Bichi a Jihar Kano ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Dattawa.
Sanata Barau Jibrin na APC da ga Kano ne ya shigar da wannan ƙudiri a gaban majalisar.
Barau a muhawarar da ya gabatar ya ce akwai bukatar a samar da tsari mai karfi a fannin ilimi ta hanyar samar da ƙarin cibiyoyin horar da malamai.
A cewarsa, makasudin kafa jami’ar ilimi ta tarayya da ke Bichi ita ce karfafa ci gaban koyo ga kowa da kowa ba tare da nuna bambancin launin fata, akida, jinsi ko siyasa ba.
“Don haɓakawa da samar da shirye-shiryen ilimi, fasaha da kuma wasu kwasa-kwasai na ƙware wa, digirin farko da karatun digiri na biyuƙwararru waɗanda ke haifar da bayar da takaddun shaida, digiri na farko, binciken karatun digiri na biyu, difloma da sauran su.
“Haka kuma zai samar da daidaiton ci gaban ilimi a jihar Kano da ma ƙasar baki daya,” in ji shi.
An zartar da kudirin ne a karatu na biyu lokacin da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya kada kuri’a.
Daga nan Lawan ya mika kudirin dokar ga kwamitin majalisar dattawa kan ilimin manyan makarantu da TetFund don karin bayanai na majalisa.