Home Labarai Umahi ya dakatar da Babban Sakatare sakamakon satar man dizel

Umahi ya dakatar da Babban Sakatare sakamakon satar man dizel

0
Umahi ya dakatar da Babban Sakatare sakamakon satar man dizel

 

 

Gwamnatin jihar Ebonyi ta dakatar da Godwin Nwankwo, Babban Sakatare na ma’aikatar wutar lantarki da makamashi, bisa zargin satar man dizal da ake tanada don fitilun kan titi.

Uchenna Orji, kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a ne ya shaida wa manema labarai a jiya Laraba a karshen taron majalisar zartarwar jihar.

Orji ya ce an kuma dakatar da Emmanuel Nwangbo, mataimaki na musamman ga gwamnan kan ayyukan jama’a a kan wannan batu.

“Majalisar ta amince da dakatar da jami’an biyu wadanda ke da alhakin kula da hasken fitilun titi a karkashin ma’aikatar,” in ji shi.

“Majalisar ta kuma samu rahoton satar dizel da ake ci gaba da yi kuma ta lura da yawan abubuwan da aka yi hasarar mutanen da ke kula fitilun kan titi.

“Saboda haka, majalisa ta yanke shawarar cewa sun yanke shawarar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) su binciki wadanda ke da kula da harkokin fitilun kan titi domin bankado masu laifin.

“An umurci shugaban ma’aikatan jihar da ya binciki ma’aikatan ma’aikatar da ke da hannu a cikin satar tare da daukar matakan da suka dace kamar yadda dokokin ma’aikatan suka bukata.”