Home Kanun Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan ta’adda sun kashe ɗan majalisa a Kaduna

DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan ta’adda sun kashe ɗan majalisa a Kaduna

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴan ta’adda sun kashe ɗan majalisa a Kaduna

 

Ƴan ta’adda masu garkuwa da mutane sun hallaka ɗan majalisar jiha, mai wakiltar mazaɓar Giwa ta, Rilwanu Gadagau, a Jihar Kaduna.

Tun da fari, an ɗauke dan majilisar ne l, wanda shine Shugaban kwamitin harkokin ƙananan hukumomi a yankin Dindin Rauga a kan titin Kaduna-Zariya a ranar Litinin da daddare.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa ƴan ta’addan sun kashe ɗan majalisar ne a kan hanyar su ta zuwa maɓoya a cikin daji.

Wata majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa maganar sa ta ƙarshe da Shehu Yunusa ya yi, ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kubau kafin harin ya faru.

“Sun yi magana da Shehu Yunusa a waya kuma maganar ma a kan rashin tsaro su ka yi ta. Yana ma tantamar shigowa Kadunan ko Zariya kawai sai ya name uzuri ya kashe wayar.

“Tun Litinin da daddare wayar da a kashe. A cikin jeji a ka tsinci gawarsa da safe,” inji majiyar.