Home Ƙasashen waje DA ƊUMI-ƊUMI: Za a yi aikin Hajjin bana tare da ƴan ƙasashen waje — Saudiya

DA ƊUMI-ƊUMI: Za a yi aikin Hajjin bana tare da ƴan ƙasashen waje — Saudiya

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Za a yi aikin Hajjin bana tare da ƴan ƙasashen waje — Saudiya

 

Ƙasar Saudi Arebiya ta tabbatar da cewa za a yi aikin Hajjin bana tare da alhazzai da ga ƙasashe a faɗin duniya.

Shafin yanar gizo na Haramain Sharifain ne ya wallafa sanarwar a yau Lahadi, inda ya baiyana cewa Ma’aikatar Hajji da Ummara za ta ware adadin alhazan ko wacce ƙasa.

Bayan an shafe shekaru 2 ba a yi aikin Hajjin da ƴan ƙasashen waje ba sakamakon annobar korona, a bana, Masarautar Saudiyya ta baiyana cewa alhazai da ga ƙasashen waje za su yi aikin Hajji.

Sai dai Ma’aikatar ta shimfida sharadi cewa kowanne maniyyaci sai ya yi allurar rigakafin korona sannan zai samu damar zuwa.