
Yayin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara Maiduguri a yau, Boko Haram sun harba roka a filin jirgin sama na Ngomari a yau.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa roka ɗaya ya sauka ne a yankin Ajilari kusa da filin jirgin sama inda sansanin sojoji ya ke.
Wata majiya ta ce mutum ɗaya ya rasu a Ngomari, inda wasu kuma su ka samu raunuka a Ajilari.