Home Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS ta ƙi amincewa da tsarin miƙa mulki ga farar hula da sojojin Nijar su ka sanar

DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS ta ƙi amincewa da tsarin miƙa mulki ga farar hula da sojojin Nijar su ka sanar

0
DA ƊUMI-ƊUMI: ECOWAS ta ƙi amincewa da tsarin miƙa mulki ga farar hula da sojojin Nijar su ka sanar

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi watsi da shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula a Nijar na shekaru uku.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa ne ya bayyana haka yayin wata hira da BBC a yau Lahadi.

Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar, ya bayyana a wani gidan talabijin da a daren jiha Asabar cewa, sojojin kasar za su mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru uku masu zuwa.

Sai dai a cikin hirar Abdel-Fatau Musa ya yi, ya ce wannan mataki na Janar Tchiani wata yaudara ce kawai wajen kawo nakasu a tattaunawa da diflomasiyya.