Home Kanun Labarai DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano, ƴan sanda sun garƙame ofishin lauyan da ya tsayawa ɓangaren Shekarau a kotu

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano, ƴan sanda sun garƙame ofishin lauyan da ya tsayawa ɓangaren Shekarau a kotu

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano, ƴan sanda sun garƙame ofishin lauyan da ya tsayawa ɓangaren Shekarau a kotu

 

Jami’an Ma’aikatar Ƙasa da Safiyo, gami da ƴan sanda sun garƙame ofishinNureini Jimoh, SAN, da ke lamba 16c kan titin Murtala Mohammed da ke cikin garin Kano.

A jiya talata ne dai lauyan ya tsayawa ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya samu nasara a kan tsagin Gwamna Ganduje na Jam’iyar APC a kotu, inda ta rushe shugabancin Abdullahi Abbas.

Lauya ya tabbatarwa jaridar DAILY NIGERIAN cewa jami’an sun zo sun kulle shi a ofishinsa tare da ma’aikatan sa a cikin ginin.

Ya ce “a halin yanzu da nake magana muna cikin ofishin an garƙame mu kuma da sauran ma’aikata. Bamu san ma yadda za mu fita daga ciki ba,”

Ƙarin bayani na nan tafe…