
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da ke neman a dakatar da rantsar da Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC a matsayin shugaban ƙasa.
Da kuri’u 8,794,726, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/ 657/2023, masu shigar da kara – Godiya Isaiah, Paul Audu da Anongu Moses – sun yi zargin cewa Tinubu ya yi karya a cikin form dinsa na EC9 cewa shi ba dan wata kasa ba ne.
Sun kuma yi zargin cewa zababben shugaban ya yi karya a kan rantsuwar shekarunsa.