
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyar sa ta yin garambawul a majalisar ministocinsa.
Shugaban ya kuma kalubalanci Ministocin da kada su kasance masu jin kunya a kafafen yada labarai, sai dai ma su fito su nuna ayyukan ma’aikatun su.
Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Laraba, Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru ya koka da cewa gwamnatin Tinubu na yin abubuwa da dama, amma ‘yan Najeriya ba su sani ba.
Ya ce, “Shugaban kasa ya bayyana aniyar sa na yin garambawul a majalisar ministocinsa kuma zai yi. Ban sani ba ko yana so ya yi kafin Oktoba, amma tabbas zai yi. Abin da zan ce ke nan, amma bai fada mana wane lokaci ne ba.”