
Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewar sa da ga jam’iyar NNPP zuwa PDP a hukumance.
Shekarau ya sanar da ficewar ta shi a wani biki da ke gudana a gidansa a Jihar Kano a yau Litinin.
Ya ce tuni ya rubuta wasika zuwa ga uwar jam’iyyar NNPP ta ƙasa, da matakin jiha, Ƙaramar Hukuma da Mazaɓa cewa ya fice da ga jam’iyar.
Ya kuma ƙara da cewa ya rubuta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, da matakin jiha cewa ya ajiye takararsa ta sanata a jam’iyar NNPP.
Shekarau ya ƙara da cewa zai iya barin jam’iyya ko sau ɗari ne matuƙar za a riƙa yin rashin adalci da zalunci a jam’iyya.
Bikin ya samu halastar Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, mataimakin takarar sa, Daniel Okowa, Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da sauran manya da masu ruwa da tsaki na jam’iyar adawa ta PDP.