
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta sanar da ɗan takarar jam’iyyar adawa ta NNPP-, Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano.
Jami’in zaɓen, Farfesa Ahmad Dokko Ibrahim ne ya ayyana Abba Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u the 1,019,602, inda babban abokin hamayyar sa, Nasiru Yusuf Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.
Karin bayani na nan tafe…