Home Siyasa DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin mataimakin takararsa

DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin mataimakin takararsa

0
DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin mataimakin takararsa

 

 

 

Rahotanni da ke iske jaridar Vanguard na nuni da cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima, tsohon Gwamnan Jihar Borno, a matsayin mataimakin takararsa.

A halin da ake ciki, Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito a yau Lahadincewa, za a gabatar da Shettima ɗin ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne shugaban jam’iyyar a mahaifarsa da ke Daura, jihar Katsina a ranar a yau.

Jaridar ta Vanguard ta kuma rawaito cewa tuni mataimakin takarar Tinubun na riƙo, Ibrahim Masari, ya janye daga zama mataimakin takarar Tinubun na riƙo.

Zaɓin Shettima da Tinubun ya yi ya tabbatar da raɗe-raɗin da a ke ta yi cewa zai zaɓi Musulmi a matsayin abokin takararsa, lamarin da wasu sassa na ƙasar su ke suka a kai.

Ƙarin bayani na nan tafe…