
Al’umma a Jihar Kano sun koka a bisa wahalar ruwan sha, musamman a ƙwaryar birnin Kano yayin da a ke azumin watan Ramadan.
Wani bincike da Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN ya gudanar, ya baiyana cewa matsalar ta fi shafar mazauna Ƙananan Hukumomi takwas na cikin ƙwaryar Kano da su ka haɗa da Dala, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Tarauni, Nassarawa da Ungogo.
Binciken ya nuna cewa mazauna Ƙananan Hukumomin sun dogara ne ga ma’aikatar ruwa ta jiha, rijiyoyin burtsatse da gwamnati da masu hannu da shuni ke samar wa sai kuma ƴan-garuwa.
Binciken na NAN ya nuna cewa matsalar wutar lantarki ta ƙasa ita ce ta haifar da matsalar, wacce ta shafi hanyoyin samar da ruwa a jihar.
Wasu mazauna jihar sun ce matsalar ruwan sha ta fi shekara 10 ta na addabar al’umma a jihar Kano, inda su ka yi jira ga gwamnatinsa ta zage dantse wajen samar da isasshen ruwan sha a jihar
Manajan-Darakta na Ma’aikatar Ruwa ta Kano, Garba Kofar-Wambai ya baiwa al’ummar jihar hakuri bisa ƙasa turp ruwan ga jama’a.
A cewarsa ma’aikatar ta dogara da wutar lantarki ne wajen sama Turi ruwan sha ga al’umma, inda ya ce faduwar layin wuta na ƙasa.
Kofar-Mata ya ce ma’aikatar ta shi za ta samar da isasshen ruwan sha da zarar an gyara wutar.