
Adadin ƴan jarida da aka kashe a faɗin duniya ya karu zuwa 86 a 2022daga 55 a 2021, wanda ke nuna karuwar kashi 36 cikin 100, kamar yadda kungiya mai kula da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ruwaito a jiya Litinin.
Fiye da rabin kisan ya faru ne a yankin Latin Amurka da Caribbean, inda aka kashe akasarin ma’aikatan yada labarai a Mexico, sai Ukraine da Haiti.
“Dole ne hukumomi su ruɓanya kokarinsu na kawo karshen wadannan laifuffuka tare da tabbatar da hukunta wadanda suka aikata laifin, domin nuna halin ko-in-kula shine babban abin da ke haifar da wannan yanayi na tashin hankali,” in ji Darakta Janar na UNESCO Audrey Azoulay a ranar Litinin.
Adadin ma’aikatan kafafen yada labarai da aka kashe a zahiri ya ragu daga 2018 zuwa 2021 kuma yanzu ya sake karuwa sosai, in ji shi.
Ba a kashe rabin ‘yan jaridun a lokacin da suke aikinsu ba, amma a lokacin da suke tafiya ko a cikin gidajensu, in ji UNESCO.
Wannan ya nuna cewa babu wani wuri mai aminci ga ‘yan jarida, ko da a lokacin hutun su, in ji rahoton.