Home Lafiya Ƙungiya ta raba magunguna kyauta ga masu cutar sikila a Kano

Ƙungiya ta raba magunguna kyauta ga masu cutar sikila a Kano

0
Ƙungiya ta raba magunguna kyauta ga masu cutar sikila a Kano

 

 

Kungiyar masu gabatar da shirye-shiryen al’ummaran yau da kullum, wato shirin Hatsin Bara, ta gudanar da rabon magani kyauta ga masu ɗauke da ciwon amosanin jini, wato sikila a Kano.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar, Sani Abdulrazak Darma, yace ƙungiyar ta bada tallafin ne bisa la’akari da halin da masu ciwon ke shiga na shan magani akai- akai, da kuma yawan shiga damuwa da iyayensu ke ciki na rashin kuɗin siyan magani aduk lokacin da ciwon ta tashi.

Ya ce ƙungiyar ta bijiro da irin wannan tsari ne sakamakon yawan samun masu buƙatar tallafin kudin magani da su ke zuwa gidajen rediyo a Kano don a tallafa musu.

Darma ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su samar da asibiti na musamman ga masu ciwon sikila, domin rage musu wahala.

“Lalurar amosani nin lalura ce da take bukatar kashe kudade, kuma mun fuskanci akwai mutane masu ƙaramin karfi da Allah ya jarabce su ko ya’yan su da wanann lalurar. Don haka dole suna bukatar a tallafa musu saboda halin matsi da ake ciki”. Inji Darma

Wasu daga cikin yaran da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su da godiya ha Allah da kuma wannan ƙungiyar.

“Babu shakka mun ji dadin wannan tallafi na magani da aka bamu, wanda zai taimaka mana wajen inganta lafiyar mu da kuma taimakawa iyayenmu wajen samar musu saukin kashe kudade,” innji daya daga cikin waɗanda suka amfana.