
Bashir El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kira da a soke kungiyar malaman jami’o’i, ASUU.
Bashir, wanda ya kira ASUU “Kungiyar mara amfani,” ya ce kamata ya yi a sauya kungiyar da malamai masu kula da jin dadin dalibai.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Bashir ya yi wannan tsokaci ne a wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Litinin.
Bashir ya rubuta: “ASUU kungiya ce mara amfani.
“Ya kamata a soke su kuma a maye gurbinsu da malaman da ke ba da lahani ga dalibai da kuma yadda hakan ke fassara ga makomar kasar nan.”
Wannan batu na Bashir na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta ASUU ta tsawaita yajin aikin na tsawon watanni shida.
ASUU ta fara yajin aikin a ranar 14 ga Fabrairu, 2022 don nuna rashin amincewa da rashin jituwa da gwamnatin tarayya.
Tun watan Fabrairu, hukumar ta tsawaita yajin aikin sau biyu.