
Wata ƙungiya mai rajin goyon bayan Atiku Abubakar, mai suna ‘Atiku State of Mind’ ta janye goyon bayanta ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ɗin, inda ta koma goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Kingsley Moghalu.
Hassan Ankuma, tsohon shugaban ƙungiyar na ƙasa ne ya bayyana haka a jiya Juma’a a Abuja a wani taron manema labarai da aka gudanar domin amincewa da dan takarar na ADC.
Ankuma ya ce ƙungiyar ta tafka kura-kurai a baya wajen yakin neman zaɓen ’yan takarar manyan jam’iyyun siyasar ƙasar biyu.
Ya ce ƙungiyar ba ta son ta sake maimaita irin wannan kuskuren a zaɓen 2023.
“Kuskuren da mu ka yi a baya shi ne, kullum muna neman goyon bayan ƴan takarar manyan jam’iyyun siyasa biyu kamar su kaɗai ne.
“Dogara ga wadannan fitattun jam’iyyun siyasa shi ya sa muka ci gaba da zaɓen shugabanni bara-gurbi saboda ƴan takarar irin waɗannan jam’iyyu kawai mu ka iya zaba duk da mun san ba za su iya ba.
“Kamar yadda muka saba, mun fara tafiya zuwa 2023, amma yayin da Najeriya ke kara tabarbarewa a kowace rana, mutum ya fahimci cewa akwai fargaba da yawa game da nan gaba.
“Hakan ne ya sa muka yi dogon numfashi, muka ja da baya muka sake yin nazari sosai kan zabin da ke gabanmu domin shekarar 2023 lokacin hutu ne ga Najeriya.
“Kuma a yau mun tara ko’odinetoci daga Ribas zuwa Borno da kuma daga Sakkwato zuwa Nnewi don fara wata sabuwar tafiya da ta samu sabbin bayanai da sanin ya kamata.
“Ni da tawaga ta mun sauya sheƙa daga ƙungiyar goyon bayan Atiku da aka fi sani da “Atiku State of Mind” kuma yanzu za a yi mata laƙabi da ‘Moghalu State of Mind’,” in ji shi.