Home Labarai Ƙungiyar IMN ta nemi gwamnatin Kaduna ta janye haramcin da ta sanya mata

Ƙungiyar IMN ta nemi gwamnatin Kaduna ta janye haramcin da ta sanya mata

0
Ƙungiyar IMN ta nemi gwamnatin Kaduna ta janye haramcin da ta sanya mata

Sashin Shurafa na kungiyar Islamic Movement in Nigeria, IMN, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta yi kira da a janye dokar hana ta ayyukan ta da gwamnatin jihar Kaduna ta sanya mata.

A tuna cewa gwamnatin jihar, a watan Oktoba, 2016, ta ayyana IMN a matsayin kungiyar da ba halastacciya ba.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar, tare da tabbatar da cewa dukkan mutane da kungiyoyi sun kasance masu bin doka da oda tare da bin tsarin mulkin Najeriya da kundin tsarin mulkinta.

Sai dai shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar, Aliyu Muhammad Sani ya ce kungiyar, wacce ta ke da nufin isar da sakon Annabi Muhammad (SAW), ba kungiya ce da ya kamata a dakatar ba.

Ya ce, “Tun a 2015 da abin ya faru a Zariya, mun kasa gudanar da ayyukanmu da dama, saboda rashin fahimtar da mutane suke yi mana. Wannan shi ne biki na farko tun bayan faruwar lamarin kuma muna fatan za mu ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da muke yi.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki shugaban nasu ba tare da wani sharadi ba, ta kuma bar shi ya koma rayuwarsa ta yau da kullum, yana mai cewa, “Ba za su iya hana nufin Allah ba.