Home Siyasa 2023: Ƙungiyar Musulmi ta MURIC ta caccaki INEC kan shirya taron siyasa a coci

2023: Ƙungiyar Musulmi ta MURIC ta caccaki INEC kan shirya taron siyasa a coci

0
2023: Ƙungiyar Musulmi ta MURIC ta caccaki INEC kan shirya taron siyasa a coci

Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi Allah-wadai da ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Legas (INEC) kan shirya taronta a cikin wata coci da ke Ikeja a jihar Legas.

Daily Trust ta rawaito cewa Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi Allah wadai da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, shelkwatar INEC ta Legas ta shirya wani taro a ranar Alhamis, kuma masu shirya taron sun zabi Cocin Archbishop Vining Memorial Church Cathedral, Ikeja, a matsayin wurin da za a gudanar da taron, wanda zai samu halartar kwamishinan zabe (REC), Mr. Olusegun Agbaje.

“Wannan abin takaici ne matuka. Ta yaya hukumar zabe ta INEC za ta iya daukar gidan ibada a matsayin wurin taron ta? Shin taron na bangaren Kiristoci na INEC ne ko kuwa? Shin INEC tana ganawa da membobin coci? ba za mu yarda da wannan ba.

“Zaben coci a matsayin wurin taron INEC ba abu ba ne na aiki da hankali, musamman idan aka yi la’akari da yanayin da mu ke ciki a Nijeriya a yau. A bayyane ya ke cewa fastoci Kirista suna da hannu sosai a yakin neman zabe. Da yawa daga cikinsu sun mayar da zaben 2023 ya zama fada a tsakanin su da musulmi.

“shelkwatar INEC ta Legas ta dauki matakin karya. Yin taron hukumar zabe a cikin coci kamar gudanar da shi ne a cikin sakatariyar daya daga cikin jam’iyyun siyasa.

“Me yasa za a ɗauki coci yayin da akwai ɗaruruwan wuraren tsaka tsaki a duk faɗin Legas? Shin INEC na inganta muradin cocin a zaben 2023? Shin wani nau’in haɗin gwiwa ne a cikin wasan? Dole ne hedkwatar INEC ta Legas ta tabbatar wa ‘yan Legas cewa za a kirga kuri’unsu. Muna kira ga ’yan Legas da su sa ido kan ayyukan INEC daga yanzu domin ba mu da tabbacin za ta kasance tsaka-tsaki,” inji Akintola.

Ya shawarci hedkwatar INEC ta Legas da ta kaucewa coci-coci domin gudanar da duk wani aiki da ta ke yi sai wanda ake nufi da ’yan cocin kadai da masallatai da wuraren ibada.

Ya ce INEC ba ta da ikon yin amfani da wuraren ibada wajen gudanar da ayyukansu, ya kuma bayyana fatan cewa sakatariyar INEC ta kasa da ke Abuja za ta yi taka-tsan-tsan a hedikwatar ta na Legas.