Home Ƙasashen waje Ƙungiyar ƙwadago za ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama a Tunisia

Ƙungiyar ƙwadago za ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama a Tunisia

0
Ƙungiyar ƙwadago za ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama a Tunisia

 

 

 

Ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙungiyar ƙwadago mafi ƙarfi a Tunisia ya bayyana cewa za a dakatar da tashi da saukar jiragen sama a Tunisia a ranar Alhamis wanda wannan na daya daga cikin matakan zanga-zanga kan tsare-tsaren Shugaba Kais Saied.

Ƙungiyar ƙwadago ta UGTT na neman a ƙara albashin ma’aikatan gwamnati bayan da matakin da gwamnatin Mista Saied ta ɗauka na dakatar da albashinsu.

Wannan matakin na ɗaya daga cikin hanyoyin gyare-gyare domin cimma yarjejeniya da Asusun Bayar da Lamuni na Duniya don samun bashin dala biliyan huɗu.

Ƙungiyar ta UGTT ta bayyana cewa duka ma’aikata kusan 160 za su daina zuwa aiki daga ranar Alhamis.