
Ƙungiyoyin ma’aikata biyu a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria sun bi sahun yajin aikin gargaɗi da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU ta ke yi.
Ƙungiyoyi biyun, waɗanda su ka haɗa da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i na Ƙasa da kuma ta Ma’aikatan Jami’a da ba ɓangaren Koyarwa ba, NASU, sun ɗauki matakin tafiya yajin aikin ne bayan yaron da kowacce ta yi a yau Litinin a jami’ar.
Da ya ke magana da manema labarai, Shugaban SSANU, Mohammed Yunusa, ya ce ya zama dole su shiga yajin aikin gargadin sabo da gwamnatin taraiya ta gaza cika alkawuran da su ka yi yarjejeniya da ita.
Shima shugaban NASU, Mohammed Sunusi Garba ya zargi gwamnatin kan kin biya musu bukatunsu da su ka haɗa da rashin daidaito wajen rabon alawus-alawus da kuma yadda ma’aikatan jami’a ɓangaren koyarwa ke amshe musu kason su na guraben ɗaukar aiki.
Ya kuma ƙara da ƙin biyan kuɗaɗen su na baya na albashi a kan sabon matakin albashi mafi ƙaranci a cikin dalilan da su ka sanya su tafiya yakin aikin.