
‘
Yusuf Sharada, wani hadimin Kwankwasiya da ya koma Gandujiyya ya yi ribas, ya ce ungulu ta koma gidanta na tsamiya.
Yusuf ya ce Gwamna Ganduje bai ba shi ko asi ba, kuma mukamin da ya yi masa alkawari ya yafe.
Ga jawabin da Yusuf ya wallafa a shafinsa bayan canja shawara da ya yi.
“Ni Yusuf Sharada Ina sanar da mutane cewa gaskiya ne jiya mun gana da gwamna Ganduje, bayan komawar Jagora Rabiu Kwankwaso Abuja. Ajizanci na Dan Adam ya jani ga yanke hukunci wanda bai yiwa ‘yan uwa da masoya dadi ba. Ina bawa dukkan wanda wannan abu da nayi ya batawa rai hakuri.
“Matsayar dana dauka ta samu rashin goyon bayan iyaye, ‘yan uwa da abokan arziki daga sassa daban daban na kasar nan.
“Gwamna Ganduje bai bani koda naira daya ba, kuma offer daya bani nayin aiki dashi na hakura da ita.
“Zan cigaba da yin abinda aka sanni akansa, in shaa Allah.
“Kwankwasiyya Amana!”