Home Siyasa 2023: Ƙusa a APC ya ba da gudummawar N100m don yaƙin neman zaɓen Tinubu

2023: Ƙusa a APC ya ba da gudummawar N100m don yaƙin neman zaɓen Tinubu

0
2023: Ƙusa a APC ya ba da gudummawar N100m don yaƙin neman zaɓen Tinubu

 

 

 

Wani ƙusa a jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Cross River, Ekpenyong Nsa, ya bayar da gudunmuwar katafaren gini mai ɗakuna 22 da kuma kuɗi naira miliyan 100 domin tallafa wa yaƙin neman zaben Bola Tinubu.

Nsa, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce tallafin na da matukar muhimmanci wajen marawa Tinubu baya domin samun nasarar sa a zaɓen shugaban ƙasa.

Nsa wanda ya nemi tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC a Cross River, ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa Tinubu zai gyara tattalin arziƙin ƙasar nan idan aka zabe shi.

Wannan a cewarsa, na daga cikin dalilan da ya sa ya tallafa wa Tinubu da ginin ofishin da kuma kudin domin yakin neman zaɓe.

A cewarsa, ofishin yaƙin neman zaben da ke lamba 78 Ndidem Usang Iso, a Ƙaramar Hukumar Calabar, yana da ɗakin taro, falo, wuraren ofis, dafa abinci, ofishin tsaro, ɗakunan karbar baƙi, ɗakin karatu da kuma ɗakunan hutawa.

Ya ce ginin zai kasance shekkwatar yaƙin neman zaɓen Tinubu a hukumance kamar yadda ya nema.

Yayin da yake taya Tinubu murnar nasarar da ya samu a zaben fidda gwani, Nsa ya yarda da jajircewar Tinubu wajen inganta rayuwar al’umma da samar da gine-ginen more rayuwa kamar yadda ya yi a jihar Legas.