
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Sokoto, Isah Bajini Galadanci ya tabbatar da cewa an kuɓutar da maniyatan da ƴan bindiga su ka yi garkuwa da su tare da jami’an tsaro da ke yi musu rakiya a jihar.
A cewar sanarwar da ya fitar a yau Talata, Galadanci said an kubutar da dukkan maniyyatan su ashirin da ɗaya da jami’an tsaro tare da ‘yan uwansu.
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni jami’an gwamnati sun tarbi maniyatan kuma suna jiran jirgin da zai dauke su zuwa kasa mai tsarki.
Sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana wadanda ke da alhakin ceto su maniyatan ba.
A tuna cewa a yau Talata ne a ka tashi da mummunan labarin cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da maniyyata ashirin da ɗaya a kan hanyarsu ta zuwa sansanin alhazai na jihar domin tafiya aikin hajjin bana daga Ƙaramar Hukumar Isa ta jihar.
Da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho, Babban Sakataren Hukumar jin Dadin Alhazai alhazai ta Nihar Sokoto, Alhaji Shehu Muhammad Dange ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a kauyen Gundumi tare da wasu jami’an tsaro da suka raka su da wasu ƴan uwansu da sukai musu rakiya.
Shima da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ƴan sanda a jihar ta wayar tarho, ya ce yana halartar taron karawa juna sani a jihar Kano ya jaddada cewa bai da masaniya kan abubuwan dake faruwa a jihar Sokoto.