Home Ilimi 2022 UTME: JAMB ta tsayar da 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’a

2022 UTME: JAMB ta tsayar da 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’a

0
2022 UTME: JAMB ta tsayar da 140 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’a

 

Hukumar Shirya Jarrabawar shiga Makarantun gaba da Sakandire, JAMB, ta sanar da fitar da maki 140 a matsayin mafi karanci wajen shiga jami’a na 2022 a ƙasar nan.

Hakazalika JAMB ta fitar a maki 100 a matsayin mafi karancin makin shiga makarantun kimiyya da fasaha, inda maki su ma kwalejojin ilimi maki 100 ne.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yau Alhamis a taron fitar da ƙa’idojin samar da guraben karatu da ke gudana, wanda Ministan Ilimi, Adamu Adamu ke jagoran ta a Abuja.

Tun da fari, Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oleyede ya nuna sabon mafi ƙarancin makin ga mahalarta taron.

Saɓanin na 2021, sabon mafi ƙarancin makin ya nuna cewa dukkanin makarantun gaba da sakandire na da maki irin ɗaya wajen samun gurbin karatu.

Kimanin masu neman shiga makarantun gaba da sakandare 1,761,262 ne suka nemi shiga makarantun jami’o’i ta Hukumar Shiga Makarantun gaba da Sakandare ta Bai-ɗaya, yayin da 98,270 suka nemi shiga jami’o’in kai tsaye ta hukumar.