Home Kasuwanci Faɗuwar darajar Naira a kan Dala: EFCC ta kai sumame kan kasuwannin canjin kuɗi 

Faɗuwar darajar Naira a kan Dala: EFCC ta kai sumame kan kasuwannin canjin kuɗi 

0
Faɗuwar darajar Naira a kan Dala: EFCC ta kai sumame kan kasuwannin canjin kuɗi 

 

A jiya Juma’a ne dai jami’an Hukumar EFFC su ka kai sumame kan kasuwar hada-hadar canjin kuɗi da ke Wuse Zone 4 a Abuja.

Hakazalika EFCC ta yi makamancin sumamenna sauran kasuwannin canjin kuɗi a faɗin ƙasar nan, kwanaki bayan da Babban Bankin Nijeriya, CBN ya zargi ƴan kasuwar da haddasa faduwar darajar Naira a kan Dalar Amurka da sauran kuɗaɗen kasashen waje.

Wata sahihiyar majiya a EFCC ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN cewa an kwashe satuttuka ana shirya yadda za a yi sumamen.

“Dabarar ita ce a rusa ƴan kasuwar canjin kuɗi ta bayan-fage waɗanda su ne ke ɓoye kuɗaɗen kasashen waje.

“Sai da jami’an EFCC ka kwashe makonni a na sa ido da binciken sirri, tare da sanya ido cikin sirri a kan yadda a ke hada-hadar canjin kuɗaɗen kasashen waje a kasuwar canjin ta Wuse,” in ji shi.

Majiyar ta ce bayan kammala bincike, hukumar ta gano cewa ƴan canjin ne su ke sayen Dalar Amurka da yawa da sauran kuɗaɗen kasashen waje su ɓoye.

“Irin wannan sumamen ma an yi shi a filayen jirgin sama a faɗin ƙasar nan,” in ji majiyar.