Home Labarai Faɗuwar darajar Naira ta sa an kori ɗaliban Nijeriya daga wata jami’a a Birtaniya

Faɗuwar darajar Naira ta sa an kori ɗaliban Nijeriya daga wata jami’a a Birtaniya

0
Faɗuwar darajar Naira ta sa an kori ɗaliban Nijeriya daga wata jami’a a Birtaniya

An kori wasu ɗalibai ƴan Najeriya daga makaranta tare da ba su umarnin barin Birtaniya saboda gazawa wajen biyan kuɗin makaranta, sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tasu, naira.

Hakan dai ya faru ne a Jami’ar Teesside, wadda ta dakatar da ɗaliban daga shiga aji saboda rashin biyan kuɗin makaranta a kan lokaci.

Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun shaida wa BBC cewa, matakin Jami’ar ya sanya sun ji kamar su kashe kansu, inda suka zargi jami’ar da ɗaukar mataki na rashin tausayi.

Mai magana da yawun Jami’ar ya ce rashin biyan kuɗin makaranta ya saɓawa dokar izinin zaman ƙasar, lamarin da ya sa suka sanar da hukumar shigi da fici ta ƙasar halin da ɗaliban suke ciki.

BBC Hausa